Gwamnan Bauchi Zai Mayar Da Kabarin Gwamnan Jihar na Farko Wajen Tarihi

Daga Wakilin mu:

Kabarin Gwamnan farko na Jihar Bauchi Marigayi Alhaji Abubakar Tatari Ali a garin Katagum dake karamar hukumar Zaki.

Yanzu haka Gwamnan Jiha Sanata Bala Abdulkadir Muhammad yana sake gina gidan zuwa na zamani tare da mayar da bangarensa zuwa cibiyar tarihi domin raya gudumowar marigayin a fannin gina kasa.

Tatari Ali ya kasance babban Sakatare a gwamnatin tarayya kana daga bisani ya yi ritaya ya shiga siyasa a jamhuriya ta biyu ya zama Gwamnan tsohuwar jihar Bauchi a tutar NPN daga 1 ga octoban 1979 zuwa 31 ga Disamban 1983.

Ya rasu a birnin landan kana aka dawo da gawarsa gida katagum aka masa jana-iza.

Yayin ziyarar tawagar ‘yan jaridu masu duba ayyukan jiha ta ziyarci kabarin mar8gayin ta yi masa addu’a yayin da ake ci gaba da aikace-aikace a cikin gidan.

Al-umar garin Katagum sun nuna farin ciki da wannan karramawa da aka yi wa Marigayin wadda yake gwarzo a tarihin jihar Bauchi saboda dumbun ayyukan ci gaba da ya aiwatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here