Abubakar Malami Ya Fice Daga APC, Ya Koma ADC

Daga Abubakar Bashir Adam Yakasai:

Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai bayyana cewa ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin ci gaba da fafutukar ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar 2 ga Yuli, 2025, Malami ya ce ya yanke wannan shawara bayan dogon nazari da tuntuba, inda ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda ake tafiyar da mulki karkashin APC.

Ya bayyana matsalolin tsaro, hauhawar farashi, rashin aiki da gazawar gwamnati a matsayin manyan dalilan sauya shekarsa, yana mai cewa an bar talaka a cikin duhu yayin da siyasa ta mamaye komai.

Malami ya ce matakin da ya dauka ba na fushi ba ne, sai dai kishin ƙasa da burin dawo da martabar shugabanci nagari.

Ya kuma tabbatar wa da al’ummar Jihar Kebbi cewa zai ci gaba da kasancewa tare da su, yana kare muradinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here